some

BA ZATO BA TSAMMANI!

5 days ago Salim Yaya Azare

Daga Aliyu Saed Gamawa 

A matsayinka na mahaifi sai ka cewa 'yarka bani wayarki (tsahon kwana ɗaya), sai ka yi abubuwa kamar haka:

  1. Bude datarta domin ganin irin saƙonnin da suke shigowa ta kafafan sada zumunta (Social Media).
  2. Duba "Gallery" ɗinta don ganin irin abin da ta ke ajiyewa (Hotuna, bidiyo...).
  3. Sauraron irin kiran da yake shigowa wayarta (wana irin mutane ne suke kiranta).
  4. Duba "Browsing history" ɗinta don ganin mai ta ke bankadawa da shafukan da take kai ziyara.

DUK ME YA YI ZAFI HAKA...!?

Saboda fadin Allah (swt): "...Ku tseratar da kanku da iyalanku daga wuta..."Saboda fadin ma'aiki (saw): "...Dukkanku masu kiwo ne kuma kowa sai an tambayeshi dangane da abin da yake kiwo..."

Ba zaka gushe Ubangiji yana yi maka hisabi ba har sai ya tambayeka dangane da tarbiyyar ƴaƴanka.

Subscribe

Sautul Hikma TV
Sautul Hikma TV

Play Radio

Sautul Hikma Radio

Install Radio

Sautul Hikma Radio
Sautul Hikma Radio
Get it on Google Play