DA MI ZAMU TUNA KA WATA RANA
3 hours ago
Salim Yaya Azare
Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa
Yan uwa kowa ya kula da kan sa cikin yadda muke gudanar da rayuwar mu ta yau da gobe
Hakika kowacce rai sai ta dan dani mutuwa.. hakan ke tabbatar da wata rana bama nan.. sai dai ambato
Mu sani ko mutuwa bata zo maka da wuri ba, to akwai tsufa, Kuma wata rana kowa sai an ambaci tarihin sa, an bada labarin rayuwar sa
Shi dan adam baya tsira daga bakin mutane, hakan yasa kowa ana maganar sa a bayan idon sa...
Kayi rayuwa mai sauki mai dadi, yadda a ranar da baka nan, ko baka kusa za'a yi begen ka ana cewa (kai ne) ka huta, ba ana murna da cewa an huta ba
Tarihi baya mantuwa, baya tausayi, baya kara, baya tsoro, baya karya... duk abinda ka yi shi za'a rubuta a fadi, kuma da shi za'a yi maka hisabi a duniya da lahira