MAJALISAR KOLI NA ADDININ MUSULUNCI TA MAYAR DA MARTANI WA SABON SHUGABAN HUKUMAR ZABE (INEC) NA KASA
2 hours ago
Salim Yaya Azare
MAJALISAR KOLI NA ADDININ MUSULUNCI TA MAYAR DA MARTANI WA SABON SHUGABAN HUKUMAR ZABE (INEC) NA KASA
Majalisar koli na addinin Musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta yi kira ga Shugaban Kasa Tinubu ya gaggauta koran sabon Shugaban hukumar zabe na Kasa Professor Joash Amupitan daga mukaminsa saboda sharri da kazafin da ya yiwa Musulunci
Professor Amupitan ya wallafa cewa Shehu Usman Danfodio (Mujaddadin Musulunci) shine tushe kuma musababbin yaduwar ta'addanci da kisan kare dangi da ake yiwa Kiristoci a Nigeria
Bayan nazarin kalamansa na sharri da Majalisar kolin addinin Musulunci tayi, tayi kira ga Maigirma Shugaban Kasa Tinubu ya gaggauta koran wannan makiyin Musulunci daga mukaminsa na Shugaban INEC
Tace Nigeria Kasa ce wanda take da mutane mabiya addinai dabam-daban, bai kamata wanda a zahiri makiyin wani addini ne ya jagoranci hukumar da take jan ragamar zabe na Kasa ba
Majalisar tayi Allah wadai da kalaman sharri da wannan makiyin addinin Musulunci ya yiwa jihadin Danfodio, tace Danfodio bai kawo ta'addanci ba, da ilimi ya yada addinin Musulunci ba kamar yadda wannan masharranci ya bayyana ba
Muna rokon Allah Ya daukaka addinin Musulunci da Musulmai, Ya kare Musulunci daga sharrin makiya