DAN ADAM BA'A IYAR MASA
2 hours ago
Salim Yaya Azare
DAN ADAM BA'A IYAR MASA
Sheikh Aliyu Said Gamawa✍️
Kada bawa ya dami kansa da sai ya samu kauna da yardar da kowa da kowa, Annabawa ma ba su iya cimma haka ba.
Wanda yake kaunarka zai kalli abin da ka yi ya Yaba Kuma ya ga ya yi kyau, wanda baya kaunar ka kuwa ba zai ga mai kyau daga gareka ya yaba ba, hasali ma sai yaga ya kai karshen muni.
Idan abu mara kyau ya same ka sai mai sonka ya ce: Jarrabawa ce. Wanda ba ya sonka kuwa sai ya ce: Allah ne Ya kama shi.
Mafi girman jarrabawa ga bawa shine wadda yawan aikin lafin sa na sa6o ya jawo masa aukawa bala'i da fitinar da Bata da magani sai istigfari
Allah ya bamu dacewa, amin