Hatta al-Hafiz al-Suyuɗiy ya tabbatar da cewa: Sufaye suna cikin masu ƙirƙirar Hadisan ƙarya, kamar Rafidha ƴan Shi'a.
3 days ago
Salim Yaya Azare
Hatta al-Hafiz al-Suyuɗiy ya tabbatar da cewa: Sufaye suna cikin masu ƙirƙirar Hadisan ƙarya, kamar Rafidha ƴan Shi'a.
Daga Aliyu Muh'd Sani
To magabatan Sufaye sun ƙirƙiri falalolin ƙarya, har da na rashin hankali, sun danganta su ga Annabi (saw), -wai- a matsayin yabo gare shi.
Kwana biyun nan na ji wani Malamin Ɗariƙa, mai yin rawani mai tsini, a Kaduna yake, yana cewa: -wai- sama kan Annabi ne.., ƙasa kazansa ne.., rana kazansa ne.., wata kazansa ne...
Duwatsu ƙashinsa ne...
Don Allah ina yabo a nan?!
Gaba ɗaya ya mayar da dukkan halittu su ne Annabi (saw). Daga ƙarshe kuma a ce: Annabi hasken Allah ne. Ka ga an mayar da komai ya zama ɗaya, komai Allah.
To idan ka zo ka ce: wannan ƙarya ne.
- Aibanta Annabi (saw) ne..
- Ƙasƙanta Annabi ne...
- Babu wata falala a cikin waɗannan maganganu, sai suka...
- Babu wani yabo a ciki sai zambo...
Sai su ce: ka zagi Annabi...
Ka aibanta Annabi...
Ka yi "su'ul adabi" ga Annabi (saw)...
Haba ku kuwa...!
Wato hujja ta ƙare sai sharri ko?!
Kuma in za a yi sharrin ma sai a mayar da Annabi (saw) shi ne abin wasanku...?!
Ta gefe guda kuma, za ka karanta Hadisi ingantacce a cikin Sahihul Bukhari da Muslim, amma sai su ce: ya taɓa janabin Annabi (saw), don haka ƙarya ne, ko a jefar da shi.
Ka duba ka ga yadda Shaiɗan yake wasa da hankulansu; ya saka su ƙaryata gaskiya, da gaskata ƙarya, kamar Rafidha ƴan Shi'a.
Allah ya shiryi waɗannan mutane.