some

*HUKUNCE HUKUNCEN RUƘIYYAH TA SHARI'A* 1️⃣5️⃣

an hour ago Salim Yaya Azare

*HUKUNCE HUKUNCEN RUƘIYYAH TA SHARI'A* 1️⃣5️⃣


???? *YADDA AKE KAMUWA DA KAMBUN BAKA:-* Ana kamuwa ne da kambun baka alokacin da shi mai wannan kambun bakan yaga abinda ya burgeshi ya kuma yabeshi, sai wannan wannan gurɓatacciyar zuciyar tashi ta fesa dafinta haɗe gubar dake cikin idanunsa akan abinda ya kalla, shiyasa Allah ya umarci Annabinsa Sallallahu alaihi Wasallama da ya nemi tsari da mai hassada, domin duk wani mai kambun baka mai hassada ne amma ba duk mai hassada bane mai kambun baka, kasantuwar cewa mai hassada shine kan gaba shiyasa akayi umarni da neman tsarinsa. 

     


        Kuma ita kambun baka wata kifiyace mai dafi da take fita daga idanu da zuciyar mai hassada ta tunkari wanda ake yiwa hassadan, wani lokaci ta sameshi wani lokaci kuma ta kuskure bata ssmeshi ba, idan ta samu mutumin da yake azkar yake Addu'o'i sai ta kauce masa, amma idan ta samu wanda baya azkar sai tayi masa tasiri.

زاد المعاد


Shaikh Abdulmuhsin Abbad Hafizahulllah yake cewa "Ana kamuwa ne kambun baka daga wurin wanda yake da wani abu na hassada atattare dashi, alokacin da ya kalli abu sai cuta ta kama abun da ikon Allah da kuma yardarsa, kuma wani lokaci kambun baka yana kaiwa ga halaka ko mutuwar wanda ya kamu dashi".

شرح سنن أبي داود ٣/٤٣٧

     

  Sannan kuma Shaikh yace "Mutum zai iya kamuwa da kambun baka daga abokinsa wanda baya masa hassada (idan yaga abinda ya burgeshi kuma baisa albarka ba) amma galibi kambun baka yana zuwane da wani abu na hassada atattare dashi".

شرح سنن أبي داود ١٦/٤٣٨


???? *SHIN ZA'A IYA KAMUWA DA KAMBUN BAKA DAGA MAKAHO??* 

 

 

 Ibnul Qayyim Allah ya masa rahama yake cewa "Tasirin kambun baka baya tsayuwa akan kallon abu kaɗai, bal zai iya yiwuwa daga makaho ma idan aka siffanta masa abu, sai zuciyarsa ta kamu da son wannan abun ko kuma abun ya burgeshi koda kuwa bai ganshi ba, kuma ma ai dayawa daga cikin wanda suka kamu da kambun baka sun kamu dashi ne ba ta hanyar kallo ba sai ta hanyar siffantawa".

الطب النبوي ١/١٢٣


???? *SHIN MAI KAMBUN BAKA YANADA ZUNUBI??* 

 

  Shaikh Saleh Alfauzan Hafizahulllah yake cewa "Idan har da gangan yayi masa kambun bakan to yanada zunubi, kuma har malaman fiqhu suna cewa idan da zai kashe mutum da kambun baka kuma ya tabbatar cewa shi yayi kuma da gangan to shima za'a kashe shi domin kisane na ganganci yayi".


???? *ABUNDA YA KAMATA MAI KAMBUN BAKA YAYI* Shaikh Ibnu Baaz Allah ya masa rahama yana cewa "Aduk lokacin da mutum yaji tsoron kambun bakan sa to kafin yace komai akan abunda ya burgeshi to ya fara da sanyawa abun albarka, kamar yace; Allah kayiwa wane Albarka, ko yace Masha Allah La quwwata illa billah, yin haka yana daga cikin sabubban samun kuɓuta daga kambun bakan".


       Rubutu na gaba zamu ambato wasu hanyoyi da basu halattaba na maganin kambun baka, in sha Allah.


*Ranar Alhamis*

*28-10-1447 =16-04-2026*


???? Don tambaya ko ƙarin bayani: Julaibeeb herbal and Islamic medicine 08160287418


???? Domin samun karatukan Malam, ku kasance tare da mu a Zauren Ɗaliban Sunnah.

Subscribe

Sautul Hikma TV
Sautul Hikma TV

Play Radio

Sautul Hikma Radio

Install Radio

Sautul Hikma Radio
Sautul Hikma Radio
Get it on Google Play