Daga: As Professor Jamilu Zarewa
1. Ya kamata malamai da Daliban ilimi su kiyaye mutuncinsu.
2. Muslim - Muslim ba shi da alaka da addini, siyasa ce kawai da kuma lissafin yadda za a ci zabe.
3. Duk Wanda zai tallata wannan Gwamnatin ya ji tsoron Allah, kuma ya san zai maimata abin da ya fada a gaban Allah.
4. Kusukure ne idan aka zagii malamin da ya zunduma kansa a SIYASA ace an taba sddini saboda Neman Duniya ya je.
5. Duk malamin da aka ba shi kudi saboda tasirinsa , ya wajaba ya samma mabiyansa, in ya ci shi kadai ya ci haramun.
6. Siyasar Nigeria Kazama ce, ya kamata magada Annabawa su yi ta da takatsantsan.
7. Babu laifi Malami ya shiga SIYASA in ya yarda da Capacity nasa..
8. Inda yanayi yana jin wa'azinmu akan WADATAR ZUCI da ba a samu ruwan koramar da zai gangara cikin kogi ba.
9. Babu laifi malami ya zunduma cikin siyasa in ya gamsu zai kawo gyara ko kuma mafi rinjayan zato.
10. Abin da ya fi kamata ga Malamin addini shi ne ya zama uba, in ya samu Mai dama-dama a cikin dalibansa ko wadanda ya sani ya dafa musu.
11. Tun da jimawa Kiristoci suka yi Gum, saboda sun fahimci, ba addini aka nufa ba a Muslim - Muslim .
12. Aliyu bn Abdullaziz Aljurjani a karni na hudu yana cewa : "Ba duk walkiiyar da ta haska take jan hankalina ba, ba duk wanda na hadu da shi nake gamsuwa zai jika ni ba"..