some

MATASHIYA

an hour ago Salim Yaya Azare

MATASHIYA:


Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa 


1. A rayuwa ana son bawa yayi haƙuri. Mu Sani duk abin da bawa ke ciki Allah yana ganin mu.


2. Mu Sani wahala ba ta dauwama, amma ladan haƙuri yana dauwama, hakuri shine maganin zaman duniya


3. Bawa ya kula da ibada musamman sallah da addu’a, domin Allah ba Ya mantuwa. Allah Yana albarka ga rayuwar masu kula da addini


4. Kada zuciya ta Kai Mutum ga aikata haramun, duk halin da Mutum ke ciki wata rana zai wuce, hakika tare da wahala akwai sauƙi.


5. Idan Allah Ya jiɓanci lamuranka, zai sauƙaƙa maka duk wani abu mai wahala. Hakika ba mai iya bayarwa ko hanawa sai Allah, don haka mu dogara ga Allah shi kadai


6. Muna rokon Allah Ya tafiyar da rayuwar mu a tsari, kuma Ya cika mana abin da muka ɗauka ba zai yiwu ba.

Ya Allah, Ka jiɓanci lamarinmu, amin.

Subscribe

Sautul Hikma TV
Sautul Hikma TV

Play Radio

Sautul Hikma Radio

Install Radio

Sautul Hikma Radio
Sautul Hikma Radio
Get it on Google Play