HUKUNCIN PHOTOGRAPH DA VIDEO:
Dada Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
1. Bayan nazarin nassoshin Shari’ar Musulunci da suka tabbata a cikin littattafan Hadithan Manzon Allah mai tsira da aminci tare da iyalansa, muna ganin Shari’ah ba ta haramta Photograph da Video ba; domin cikin yin su babu kwaikwayon halittar Allah mai rai irin na mutane, kamar yadda wannan ma’anar take cikin zanawa da hannu ko kerawa, ko sassakawa saboda su wadannan su ne wannan ma’ana ta kwaikwayon halittar Allah ke cikinsu. Waalhu A’alam.
2. Mun kai ga fahimtar cewa shi Photograph da Video yana fitar da jikin mutum ne kamar yadda Allah ya halicce shi ba wai kwaikwayo yake yi ba, tamkar dai irin yadda madubi yake yi, shi kuwa madubi Shari’ar Musulunci ba ta haramta amfani da shi ba; saboda babu kwaikwayon halittar Allah mai rai irin na mutum cikin yin amfani da shi.
3. Muna sane da cewa da yawa daga cikin Malumanmu masu daraja sun haramta Photograph, akwai ma ‘yan kadan daga cikinsu da suka haramta Video kamar Sheikh Nasurudden Al-Abaniy. Amma tabbas mun ga kuren ijtihadinsu muna kuma rokon Allah Ya ba su ladan da yake ba wa mujtahidin da ya yi kure.
4. Amma abin da nake yawan mamakin sa shi ne fahimtar wanda yake haramta Photograph sannan kuma ya halatta Video, tabbas wannan mutum ina mamakin irin yadda wannan fahimtar tasa ta kasance haka.
JIBWIS NIGERIA ????????