some

Ƙungiyar IZALA ta jajantawa al'ummar garin Maiduguri bisa ambaliyar ruwa da ya afka musu

23 days ago Abdussalam Auwal

Ƙungiyar wa'azin musulunci ta Jama'atu Izalatil Bid'ah wa iƙamatis Sunna (JIBWIS) ta jajantawa gwamnatin jahar Borno, masarautar Borno da al'ummar garin Maiduguri da kewaye, bisa Ibti'la,in ambaliyar ruwa da ya afka musu daga Alo Dam anan birnin Maiduguri da kewaye.

Shugaban JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau a madadin ƙungiyar shi ya fitar da saƙon jajen inda ya tausayawa al'ummar da lamarin ya shafa.

Sheikh Bala Lau, ya jajanta tare da addu'oin Allah ya kiyaye faruwar hakan a gaba, waɗanda sukayi asara da dukiya, motoci da Babura Allah ya maida musu, waɗanda suka Rasa ran su kuma Allah ya jiƙansu ya gafarta mu.

A ƙarshe shugaban yayi ƙira ga gwamnatin tarayya Dana jahar Borno da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen daƙile afkuwar hakan a gaba, tare da tallafawa waɗanda lamarin ya shafa a matakin taimakon farko.