some

Maganar rashin bin Musulmi Sallah

2 hours ago Salim Yaya Azare

Maganar rashin bin Musulmi Sallah


Daga Aliyu Muh'd Sani

 

 yana daga cikin abubuwa da masu kiran hadin kan Kungiyoyi suke sukar Wahabiyawa da shi, wato su Prof. Maqari, Dr. Gumi d.s, saboda Wahabiyawa ba sa bin 'yan Bidi'a Sallah (Sufaye 'yan Shi'a, 'yan Tatsine d.s), alhali abu ne da yake tabbatacce a Mazhabarmu ta Malikiyya. Idan ka koma cikin "Mukhtaswar" za ka ga inda Shaikh Khalil ya ce:


"وأعاد بوقت في: كحروري".


مختصر خليل (ص: 40)



"Ya rama Sallah a cikin lokaci idan ya bi dan Bidi'a Sallah, kamar dan Haruriyya (Bakhawarije)".


Sai Shaikh Dardeer a sharhinsa ya ce:


(وأعاد بوقت) اختياري (في) اقتداء بإمام بدعي مختلف في تكفيره والأصح عدم الكفر (كحروري) وقدري.


والحرورية قوم خرجوا على علي - رضي الله عنه - بحروراء قرية من قرى الكوفة على ميلين منها نقموا عليه في التحكيم وكفروا بالذنب


Sai ya kara har da Baqare, mai inkarin Kaddara, wato Mu'utazilawa da 'yan Shi'a.



Kuma fa sun ambaci dan Haruriyya da dan Qadariyya ne a matsayin misali ne. Don haka duka 'yan Bidi'a irinsu haka za a mu'amalance su, idan an bi su Sallah cikin rashin sani, sai aka samu labari daga baya, to za a rama Sallar.


Kai, ba kawai bin Sallah ba, hatta kauracewa, ga abin da mai Risala ya ce:


"والهجران الجائز هجران ذي البدعة".


الرسالة للقيرواني (ص: 153)



"Kauracewa da ya halasta shi ne kaurace wa dan Bidi'a".


Don haka batun kaurace ma 'yan bidi'a, da rashin binsu Sallah, magana ce ta Fiqhu ba kawai ta Wahabiyanci ba. Ga dai abin da Mazhabar Malikiyya take kai.


Saboda haka, su masu neman hadin kai, yaya za mu da wannan karatun?