05 AQEEDATUT TAUHID
Aug 27, 2025
MATASHIYA (Kwanciyar Kabari):
Daga Sheikh Aliyu Said Gamawa
Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Lallai ƙabari shi ne masauƙi na farko a rayuwar lahira. Duk wanda ya tsira a ƙabari to abin da zai biyo ba ya (na hisabi) zai zama da sauƙi. Wanda kuwa bai tsira a ƙabari ba, to abin da zai biyo (na hisabi) ba ya zai fi na ƙabarin tsanani.”
[Sahihu Tirmidhi: 2308]
ABUBUWAN DA KE JAWO AZABAR KABARI:
1. Barci akan sallah da ganganci
2. Taurin biyan bashi da gan-ganci
3. Zama cikin rashin ingataccen tsarki
4. Kasa amsa tambayar kabari
5. Annamimanci
6. Kin biyan hakkin mai kodago da ganganci