MAZHABA DA MAZHABANCI
an hour ago
Salim Yaya Azare
MAZHABA DA MAZHABANCI
Daga Dr Uthman Ibrahim Giade Abuhibah
Manyan Malamai na da Dana yanzu duk suna da mazhaba Ibn taimiyya Ibn Baz Ibn Uthaimeen Albani (Rahimahumullah) duk sunyi Kuma sunce ya halatta a yi riko da mazhaba
Ta'assubanci suka hana ba mazhaba ba,
shi kuma Ta'assubanci a kan same shi ko babu mazhabar ma
Ni fa ban San wani malami da ya soki riko da mazhaba ba,
Kai dole ne ma a fara karatu da mazhaba Dan
ita fa mazhaba makaranta ce Dan haka kafin mazhabobi 4 ma a kwai mazhabobin Sahabbai da tabi'ai Sai dai su 4 din ne suka fi yaduwa da kuma wanzuwa.
Duk Magabata sun yi mazhaba wasu daga baya su kai matsayin tsayuwa da kafarsu amma Mafi yawa ba sa iya kai wa hakan.
Dan haka fada da mazhaba fada da Addini ne a kula da kyau.
In baka yi mazhabar Magabata ba to ko shakka babu ka bi mazhabar malaman da ka yarda da su ita ma mazhaba ce ta raunana ma kuwa.