03 Da'aful Iman
Aug 14, 2025
✍???? Sheikh Aliyu Said Gamawa
Wata rana Abu Ishaƙ As-sab'i ya fashe da kuka, sai a ka tambayeshi menene ya sanya shi kuka?! sai ya ke cewa: ƙarfi na ya ƙare ban iya yin salla a tsaye!, Babu abinda nake iya karantawa sai surori biyu baƙara da Ali-imran.
Mu kuma a yanzu munyi rauni, lalaci ya baibaye jikkunan mu, ma su rabo daga cikin mu suke yin SALLAR DARE.
Muna da dama, lokaci, lafiya, ƙarfi, muyi amfani da su wajen yin ibadar Allah, kamin lokacin da tsufa ko mutuwa zasu riske mu daga nan sauran dama ta yanke gare mu.
Muyi Amfani da lafiyar mu, da damar mu wajen yin ibadar ALLAH