some

Sheikh Abubakar Gumi: Malamin da ya sauya tunanin Musulman Najeriya game da ibada

14 hours ago Salim Yaya Azare

Sheikh Abubakar Gumi: Malamin da ya sauya tunanin Musulman Najeriya game da ibada


Abubakar Gumi: Malamin da ya sauya tunanin Musulman Najeriya game da ibada


Sheikh Abubakar Gumi, sanye da rawani mai ratsin ja da fariAsalin hoton,FB/Ahmad Abubakar Gumi


Bayanan hoto,Sheikh Abubakar Gumi ya jagoranci kawo sauyi a daidai lokacin da akasarin al’ummar Musulmin Najeriya ke ‘cakuda ibada da wasu ayyukan da suka saba da tanadin al-Kur’ani da hadisai’


Da ya sauya tunanin Musulman Najeriya game da ibada

Karanta rubutu kawai domin rage cin data

Sheikh Abubakar Gumi, sanye da rawani mai ratsin ja da fariAsalin hoton,FB/Ahmad Abubakar Gumi

Bayanan hoto,Sheikh Abubakar Gumi ya jagoranci kawo sauyi a daidai lokacin da akasarin al’ummar Musulmin Najeriya ke ‘cakuda ibada da wasu ayyukan da suka saba da tanadin al-Kur’ani da hadisai’



"Lokacin da muka je wurin jifan shaiɗan (Jamra) sa'ilin aikin Hajji, sai mutanenmu suka riƙa yin wasu abubuwa marasa ma'ana.


"Wasu suka riƙa nemo manyan duwatsu, wasu kuma suka riƙa cire takalmansu suna jifan jamrah, suna zage-zage da furta munanan kalamai, da sunan jifan shaiɗan."


Wannan na daga cikin abubuwan da suka sanya Sheikh Abubakar Gumi ya yi yunƙuri a hukumance na sake faɗakar da mabiya addinin Musulunci a Najeriya yadda ake yin addini, bayan sanar da Firimiyan arewa na farko Ahmadu Bello, kamar yadda ɗaya daga cikin manyan ɗaliban marigayin, Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun ya tabbatar wa BBC.


Wannan yunƙuri ya haifar da kafa wasu ƙungiyoyi guda biyu waɗanda suka jagoranci tafiyar da lamurran addinin Musulunci a Najeriya - Jama'atu Nasril Islam, sai kuma daga baya Jama'atu Izalatil Bidi'a wa Iqamatussunnah - lamarin da ya yi tasiri kan miliyoyin mabiya addinin a Najeriya.


Shekara 33 bayan rasuwarsa, miliyoyin Musulmai a Najeriya na ci gaba da bin koyarwarsa, sannan ƙungiyoyin da ya jagoranci kafawa ne a gaba-gaba wajen yaɗawa da kuma tafiyar da al'amuran Musulunci a ƙasar.


Baya ga Shehu Usman Danfodiyo, wanda ya yi jihadin sake ɗabbaƙa addinin Musulunci a ƙasar Hausa a farkon shekarun 1800, ana ganin cewa babu wani malami da koyarsa ta Musulunci ta yi tasiri a Najeriya kamar Abubakar Gumi.


Wasu masana addini ma na ganin tasirin da Gumi ya yi "ta fi" ta Usman Danfodio, kasancewar a lokacinsa akwai hanyoyin sadarwa irin su talabijin da rediyo da hanyar wallafa litattafai da jaridu, waɗanda suka taimaka wajen yaɗa ayyukansa a ƙasar Hausa da maƙwafta.


    Kawo sauyi


Tun kafin yunƙurin samar da ƙungiyoyin sake ilimantar da Musulman Najeriya kan ibada, Abubakar Gumi ya kasance mutum mai neman kawo sauyi, lamarin da ya sa ya yi ƙaurin suna tsakanin malamai da sarakuna har ma da turawan mulkin mallaka.


A cikin littafinsa na Manufata, Gumi ya tuno yadda ya ƙalubalanci malaman addinin Musulunci waɗanda suke yin addini "yadda suka ga dama".


Gumi ya ce "Sufanci ya zamo jiki a tsakanin al'umma ta yadda babu wanda ya damu ya binciki ko ya yi daidai da koyawar al-Ƙur'ani da hadisan annabi Muhammad".


Irin wannan yunƙuri nasa ya fara jan hankali ne a lokacin da yake koyarwa a wata makaranta da ke Maru a shekarar 1949. A lokacin ya fahimci yadda malaman addini da kuma sauran al'umma ke cakuɗa ibada da al'adu ko wasu abubuwa na daban.


Limamin Juma'a na Maru a wancan lokaci ya kasance yana yin taimama domin yin sallah a maimakon alwala da ruwa, duk kuwa da wadatuwar ruwan da kuma rashin wata hujja ta yin taimamar.


Bayan yunƙurin da ya yi na faɗakar da limamin game da 'haramcin' hakan, amma abin ya ci tura, Gumi ya hana ɗalibansa halartar sallar Juma'a a babban masallacin Maru, inda ya riƙa jan su sallah a cikin makaranta.


A matsayin martani, sarkin Maru ya rubuta takardar ƙorafi kan Abubakar Gumi zuwa ga fadar sarkin Musulmi da kuma hukumomi turawan mulkin mallaka.


Sai dai a ƙarshe Abubakar Gumi ne ya yi nasara ta hanyar gabatar da hujjoji masu ƙarfi da suka tabbatar da koyarwarsa.


A game da turawan mulkin mallaka, Gumi ya ce "Idan na tuna ɓarnar da mulkin mallakar Birtaniya ya yi a ƙasarmu, nakan riƙa mamakin yadda mutanenmu suka kwashe tsawon shekaru ba tare da sun fahimci hakan ba.


"Hatta a tsakanin masu iliminmu, ƙalilan ne suke tsayawa su fahimci yadda mulkin mallaka ya illa ga tunaninmu". 

  


          Littafin da ya yamutsa hazo



Littafin da Abubakar Gumi ya rubuta a shekara ta 1972 mai taken 'Al-Aqida al-Sahiha bi-Muwafaqat al-Shar'i' ya haifar da zazzafar muhawara tsakanin Musulman arewacin Najeriya sanadiyyar kakkausar sukar da littafin ya yi kan wasu ayyuka na masu bin akidar sufanci.


A wannan lokaci kusan ɗaukacin Musulman Najeriya na bin tsari ne na ɗariƙa, wadda ta samo asali daga koyarwa irin ta sufanci.


Da farko Abubakar Gumi ya ce ya rubuta littafin ne domin amfanin masu ilimi, kasancewar koyarwar littafin zai yi tsaurin fahimta ga mabiya, waɗanda iliminsu bai yi nisa ba.


Sai dai a lokacin da ya tafi Saudiyya, sai Mallam Isma'ila Idris ya ɗauki littafin ya yi wa'azi da shi a birnin Kaduna, wani abu da ya haifar da ruɗani, abin da ya kai ga dole sai da ya ajiye aikinsa na gwamnati a matsayin malami.


Bayan ajiye aiki, Mallam Idris ya shiga aikin soja, inda ya yi aiki a garuruwa da dama na Najeriya, kafin mayar da shi garin Jos, kuma duk inda ya je ya riƙa koyar da karatu ta hanyar amfani da littafin Sheikh Gumi na 'Al-Aqida al-Sahiha'.


Wannan ne ya haifar da ƙaddamar da ƙungiyar Izalatil Bidi'a wa iƙamatussunnah a birnin Jos.


Da'awar Gumi na kira ga Musulmi su yi aiki da karantarwar al-Ƙur'ani da kuma Hadisan Annabi Muhammad (S.A.W) kawai, wani abu da ake ganin ya kawo gagarumin sauyi a yadda ake tafiyar da ibada a Najeriya da wasu ƙasashen da ke maƙwaftaka a lokacin.



      Wane ne Abubakar Gumi?



An haifi Abubakar Mahmud Gumi ne ranar Juma'a 7 ga watan Nuwamban shekarar 1924, wadda ita ce Juma'a ta ƙarshe ta watan Ramadan na shekara ta 1344 bayan hijira, kamar yadda malamin ya bayyana a cikin litattafinsa.


Shahararren malamin addinin Musulunci ne kuma masanin shari'a, wanda ya kai har matsayin Alkalin Alkalai (Grand kadi) na arewacin Najeriya.


Ya fara samun ilimi ne a wajen mahaifinsa, Malam Mahmoud Na-Gumi.


Sunan mahaifinsa Malam Mahmoud Na-Gumi, wanda ake kiransa da Na-Gumi, saboda zaman da ya yi a garin Gumi bayan zama a wurare daban-daban na ƙasar Hausa, kamar Katsina, Borno da Dutse.


Mahaifin Abubakar Gumi ya kasance babban malamin addinin Musulunci da shari'a, kuma ɗaya daga cikin malamai da aka fi girmamawa a yankin Sokoto da Zamfara da kuma Kebbi a zamaninsa.


Kakan mahaifin Abubakar Gumi shi ne Sheikh Aliyu Barou el-Badawi, wanda ya fito daga ƙabilar Larabawa ta Bedouin, waɗanda aka sani da kiwo a yankin Larabawa da arewacin nahiyar Afirka.


Babu cikakken bayani kan yadda ya isa yankin Sokoto, amma dai ana ganin zuwan sa ba ya rasa nasaba da ziyarar da Larabawa suka riƙa yi zuwa ƙasar Hausa bayan ƙarni na 15, lokacin da Musulunci ya samu karɓuwa a ƙasar Hausa.


Sunan mahaifiyar Abubakar Gumi Hafsatu, ɗiyar Malam Adamu, wadda mahaifinsa ya aura lokacin da yake koyarwa a Jega.


        Karatu



Abubakar Gumi ya fara karatunsa ne a hannun mahaifinsa, Malam Mahmoud Na-Gumi, inda ya haddace al-Ƙur'ani sannan kuma ya yi karatun litattafai da dama.


Bayan nan a shekara ta 1933 ya shiga makarantar boko ta Dogon Daji Elementary School, inda daga baya aka mayar da shi makarantar Middle da ke Sokoto a shekara ta 1936.


Daga nan ne ya tafi makarantar ilimin shari'a ta Kano. Sannan a shekara ta 1952 ya zurfafa karatu a makarantar koyar da Larabci ta Kano.


Daga nan ne kuma ya yi karatun babbar difloma a cibiyar ilimi ta Bakht al-Rida da ke Sudan daga shekarar 1955 zuwa 1956.


A shekarar 1987, Gumi ya lashe kyautar Sarki Faisal kan hidima ga addinin Muslunci.


Daga cikin abubuwan da suka sa ya cancanci lambar girmamawar su ne wa'azi da kuma koyar da addinin Musulunci, taimakawa wajen kafa ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam da fassara alƙur'ani zuwa harshen Hausa da kuma rubuta litattafai na addinin Musulunci.


      

          Ayyukan ilimi


Abubakar Gumi ya yi gagarumar hidima ta hanyar rubuce-rubuce da kuma fassarar litattafai na addini.


Litattafan da ya rubuta waɗanda suka fi yin fice sun haɗa da:


•Tafsirin Al-ƙur'ani na Rad al-Azhan ila Ma'ani al-Qur`an


•Al-Aqidah al-Sahiha bi Muwafaqat al-Shari'a


•Kitab al-Nasihaila Amir MantiqatKatsina


•Manufata / Where I Stand


•Hal al-Niza` fi Mas´alatNuzul Isa alaih al-Salatwa al-Salam


•Musulunchi da Abinda ke Rushe Shi


•Zad al-Haj


•Kitab Maratib al-Islam


•Kitab Manasik al-hajwa al-Umra



      Fassara:


•Fassarar ma'anonin al-Ƙur'ani mai girma


•Fassarar Hadisai Arba'in (al-Nawawi)


•Fassarar littafin Nur al-Bab


•Fassarar littafin Hidayat al-Tullab fiAhamMasail al-Din



       Rasuwa


Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi ya rasu ne a ranar 11 ga watan Satumba shekara ta 1992, a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.


A lokacin da ya rasu, al'umma sun girgiza kasancerwar sa mutumin da ya samu karɓuwa a tsakanin shugabanni da masu sarauta da kuma sauran al'umma.


Gumi ya kasance malami, alƙali kuma tsani tsakanin shugabanni da talakawa.


Baya ga batun addini, Sheikh Gumi ya taka muhimmiyar rawa a ɓangaren mulki da kuma ayyukan gwamnati.


Ya kasance mai kusanci sosai ga masu mulki, sannan ya riƙa ƙarfafa wa al'ummar arewacin Najeriya, musamman Musulmai gwiwa wajen shiga ayyukan gwamnati da karatun zamani.


Tsarin koyarwarsa ya sha bamban, inda ake yaba masa wajen haƙuri tare da ƙoƙarin ganin al'umma sun fahimci abin da yake koyarwa.


✍???? BBC Hausa

Subscribe

Sautul Hikma TV
Sautul Hikma TV

Play Radio

Sautul Hikma Radio

Install Radio

Sautul Hikma Radio
Sautul Hikma Radio
Get it on Google Play